Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWani ɗan majalisa ya nemi a duba lafiyar kwakwalwar Trump kan yaƙin...

Wani ɗan majalisa ya nemi a duba lafiyar kwakwalwar Trump kan yaƙin Iran

An bukaci a yi wa Donald Trump gwajin ƙwaƙwalwa sakamakon matakan da ya ɗauka kan rikicin Iran.

Dan majalisar Amurka, Jamie Raskin, ya bukaci likitan Fadar White House da ya gudanar da gwajin kwakwalwa ga Shugaba Donald Trump sakamakon kalamansa masu tsauri kan yaƙin Amurka da Iran.

Dan jam’iyyar Democrat daga Maryland ya bi sahun wasu ’yan majalisar da suka nuna damuwa a kwanakin nan kan yadda shugaban ke tafiyar da rikicin da kuma kalamansa a bainar jama’a.

CNN ta wallafa cewa ‘yan siyasar Amurka, musamman ’yan Democrat sun fara tambayar ko Trump yana da cikakkiyar ƙwarewar da ta dace don ci gaba da shugabancin kasar.

“A cikin kwanakin nan, ƙasar ta ga yadda kalaman Shugaba Trump ke ƙara zama marasa tsari, masu karo da juna, cike da kalamai masu hadari, rudani da kuma barazana,”
In ji Raskin a cikin wata wasiƙa

Raskin ya bayar da dalilai da dama kan shakku game da lafiyar Trump, ciki har da sakon Easter da Trump ya wallafa mai cike da kalamai masu hadari yana kira ga Iran ta buɗe mashigar Hormuz.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments