Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDuk da tsadar rayuwa mu gode wa Allah saboda halin Najeriya bai...

Duk da tsadar rayuwa mu gode wa Allah saboda halin Najeriya bai kai na wasu ƙasashe muni ba – Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa duk da tsadar mai, Najeriya na cikin yanayi mafi sauƙi idan aka kwatanta da wasu ƙasashe.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ya san irin wahalhalun da ake fuskanta sakamakon hauhawar farashin man fetur, inda ya buƙaci ’yan ƙasar da su ci gaba da kasancewa masu nuna ƙarfin hali, yana mai cewa har yanzu ƙasar tana cikin yanayi mai kyau idan aka kwatanta da wasu ƙasashe.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ziyarar da ya kai jihar Bayelsa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka.

Yayin da yake tsokaci kan damuwar da ake nunawa game da taɓarɓarewar tattalin arzikin Najeriya, Tinubu ya ce, “Ina jin koke-kokenku daga fannoni daban-daban na tattalin arziki.

Farashin man fetur ya yi tsada sosai, amma ku duba wasu ƙasashe, kawai mu gode wa Allah tare cewa halin da kuke ciki ya fi na wasu kyawu.”

Tinubu ya kwatanta halin da Najeriya ke ciki da na sauran ƙasashen Afirka, inda ya bayyana cewa wannan ƙalubalen ba a nan kaɗai ya tsaya ba.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments