Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAtiku ya yi alkawarin goyon bayan duk wanda ADC ta zaba a...

Atiku ya yi alkawarin goyon bayan duk wanda ADC ta zaba a matsayin ɗan takararta

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, kuma mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa zai mara baya ga duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar, a zaben 2027.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, kuma mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa zai mara baya ga duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar, a zaben 2027.

Ya kuma yi watsi da zargin cewa INEC za ta iya hana ADC gudanar da ayyukanta, yana mai cewa jam’iyyar na kara samun mambobi a fadin kasa.

INEC dai ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da mu’amala da shugabannin ADC ba, kuma ba za ta sa ido kan babban taron jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 14 ga Afrilu ba, bisa hukuncin kotu. Sai dai ADC ta yi watsi da wannan mataki, tana mai cewa an yi kuskuren fassara hukuncin kotun.

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da shirinta na gudanar da babban taro da sauran ayyuka duk da wannan matsala.

A wata hira da ya yi, Atiku ya ce wasu masu ruwa da tsaki ne ke haddasa rikicin da ke cikin jam’iyyar saboda yadda take kara samun karbuwa.

Ya ce zai goyi bayan duk wanda ya fito a matsayin dan takara, yana mai cewa jam’iyyar na bai wa matasa da mata dama sosai a harkokin siyasa.

Ya kara da cewa yana da yakinin ‘yan Najeriya na bukatar sauyi, musamman ganin yadda matsalar tsaro da tattalin arziki ke kara tsananta.

Atiku ya danganta matsalar tsaro, musamman a Arewacin Najeriya, da rashin aikin yi da kuma rashin kulawa da ilimi, yana mai cewa gwamnati ba ta ba ilimi muhimmancin da ya kamata.

Haka kuma ya zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula kan cin hanci da rashawa, yana mai cewa wannan matsala ta yi kamari a kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments