Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban babbar kotun jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhume-tuhume da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa.
An gurfanar da El-Rufa’i ne kan zargin laifuka da suka haɗa da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, damfara, da bai wa wasu dama fiye da yadda ya dace, da kuma wasu tuhume-tuhume da suka shafi kudade.
El-Rufai ya bayyana a kotun ne bayan ICPC ta sake shi daga tsare shin da ta yi na fiye wata guda, wanda hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai, a Cairo, Masar.
Bayan kammala gurfanar da shi babbar kotun jihar, za a kai El-Rufai Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda za a fara sauraron buƙatar belinsa da ya shigar.
Ana sa ran cewa za a duba batun belinsa cikin gaggawa, saboda irin nauyin tuhumomin da ake masa.