Ƙungiyar kiristocin Najeriya CAN, ta yi Allah-wadai da kashe-kashen da suka faru a Angwan Rukuba a Jos a ranar Palm Sunday.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Daniel Okoh, ya fitar a Abuja, ya nuna damuwa sosai kan harin, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su daina maganganu kawai su ɗauki mataki na gaskiya. Ya ce dole ne a gaggauta kamo masu laifin a hukunta su.
Ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya sun gaji da jimamin mutuwa da kuma fitar da sanarwa kawai, suna buƙatar ganin an yi aiki a zahiri. Ya bayyana cewa ranar da ya kamata ta kasance ta zaman lafiya da bege ta koma ranar zubar da jini inda aka kashe maza, mata da yara.
Shugaban CAN ya kuma nuna damuwa kan rahotannin cewa wasu daga cikin maharan suna sanye da kayan da ke kama da na jami’an tsaro, yana mai cewa hakan na iya lalata amincewar jama’a ga hukumomi, don haka ya kamata a bincika sosai.
Yayin da Kiristoci ke shiga makon Holy Week, ya shawarci mabiya da su kasance masu addu’a tare da ƙara taka-tsantsan, musamman a lokacin Good Friday da bukukuwan Easter.
Ya kammala da cewa Najeriya na cikin wani lokaci mai wahala, amma ya kamata hakan ya zama darasi domin ƙarfafa tsaro da kare rayukan al’umma.