Jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta fara zagayen rigakafin cutar shan inna daga gobe Lahadi, inda ake shirin yi wa akalla yara miliyan 2.5 allura a fadin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Jami’in wayar da kai kan lafiya, Alhaji Isiah Yushau, ya ce zagayen zai gudana na tsawon kwanaki huɗu, yana mai cewa zai shafi yara daga haihuwa zuwa watanni 59 a sama da unguwanni 28,000. Ya jaddada cewa an tanadi isassun allurai, ma’aikata da kayan aiki domin tabbatar da cewa babu yaron da za a bari a baya, har ma da wuraren da ke da matsalar tsaro.
Ya ƙara da cewa wannan shiri wani ɓangare ne na kamfen ɗin ƙasa baki ɗaya da ya haɗa jihohi da dama, inda aka tattara bayanai domin inganta tsare-tsare a harkar lafiya.
A cewarsa, da farko an samu sama da lokuta 7,000 na ƙin karɓar rigakafi, amma an rage su zuwa kusan 1,000 bayan ƙara wayar da kai a cikin al’umma.
Ya kuma roƙi iyaye da masu kula da yara da su kai ‘ya’yansu domin yin rigakafi, yana mai jaddada cewa rigakafi na da matuƙar muhimmanci wajen kare yara daga cutar shan inna.