Hukumar kula da shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano (REMASAB) ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsarin sarrafa shara mai dorewa.
Ta bayyana haka ne bayan kammala wani taron bita na kwanaki biyu mai taken “buɗe damar sauya shara zuwa tattalin arziƙi a Najeriya” da aka gudanar a Kano.
Taron bitar, wanda aka yi a otal din Bristol Palace, ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki domin tattauna sabbin hanyoyi na sauya shara zuwa abin da zai amfani tattalin arziki tare da inganta kare muhalli.
A madadin Manajan Darakta na REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, Umar Dahiru ya nuna godiya ga masu shirya taron bisa zaɓar Kano a matsayin wurin gudanar da shi, yana mai cewa hakan yana da matuƙar muhimmanci ga manufofin ci gaban jihar.
“Taro ya haɗa da masu ruwa da tsaki domin nemo sabbin hanyoyin magance matsalar shara da kuma samar da darajar tattalin arziki daga gare ta,” in ji Dahiru.
Ya kuma jaddada muhimmancin shirye-shirye kamar sake sarrafa kayan roba (PREP), inda ya bayyana su a matsayin muhimman matakai wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma magance matsalolin muhalli.
Dahiru ya Kuma ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na da aniyar ɗaukar sabbin dabarun sarrafa shara a faɗin jihar.
A cewarsa, wasu daga cikin shirye-shiryen da ake aiwatarwa ko kuma ake shirin aiwatarwa sun haɗa da kafa wurin sake sarrafa shara, gabatar da wurin ajiye shara na musamman a makarantu, da kuma shirye-shiryen ƙarfafa mata ta fuskar tattalin arziki.