Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauke Alhaji shehu Wanda Sagagi daga mukaminsa Kwamishinan ma’aikatar zuba jari, kasuwanci da masana’antu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu.
Gwamnan ya umarci Alhaji Sagagi da ya mika ragamar ma’aikatar ga Babban Sakataren ma’aikatar.
Ana sa ran zai kammala mika ragamar aiki zuwa gobe da safe.
Hakazalika gwamnan, ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin.