Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiRikicin Gabas ta Tsakiya na iya dawo da tsarin yin aiki daga...

Rikicin Gabas ta Tsakiya na iya dawo da tsarin yin aiki daga gida kamar lokacin COVID19 — Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya, yana mai gargadin cewa lamarin na iya mayar da wasu ƙasashe zuwa tsarin aiki daga gida kamar lokacin COVID-19.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya, yana mai gargadin cewa lamarin na iya mayar da wasu ƙasashe zuwa tsarin aiki daga gida kamar lokacin COVID-19.

Dangote ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a gidansa da ke Lagos.Ya nuna damuwa kan yadda rashin tabbas a farashin mai ke shafar tattalin arziki, yana mai cewa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka na iya komawa tsarin aiki daga gida idan lamarin ya ci gaba.

Dangote ya yi kira da a yi addu’a tare da neman shiga tsakani na ƙasa da ƙasa domin kawo ƙarshen rikicin, wanda ya riga ya fara shafar farashin mai da sauran makamashi.

Ya ce a wasu ƙasashe ma an riga an rage kwanakin aiki ko kuma ana tilasta mutane su yi aiki daga gida saboda tsadar rayuwa. Idan lamarin bai daidaita ba, zai iya kai ga dakatar da fita aiki gaba ɗaya kamar yadda aka yi a lokacin COVID-19.

Ya kuma yi gargadin cewa wasu na iya amfani da wannan dama wajen ƙara farashi domin samun riba, wanda hakan zai ƙara tsananta halin da jama’a ke ciki, musamman ganin cewa gwamnati ba za ta iya ƙara albashi cikin sauƙi ba.

Dangote ya ce waɗanda za su fi shan wahala su ne ƙananan ‘yan kasuwa kamar masu aski, masu yin burodi da masu masana’antu da ke amfani da janareta, saboda tsadar makamashi.

Game da ziyarar da Tinubu ya kai Birtaniya, Dangote ya yaba da yarjejeniyar gina ababen more rayuwa ta fam miliyan 746 da aka cimma, yana mai cewa hakan na nuna ƙarin amincewa da Najeriya daga ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa wannan yarjejeniya na iya jawo sauran ƙasashe su biyo baya wajen saka hannun jari a Najeriya.

Dangote ya kuma bayyana cewa yanzu masu zuba jari na Najeriya za su iya samun damar amfani da cibiyar UK Export Finance, wacce ke ba da lamuni amma ba a cika amfani da ita ba a baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments