Shugaban Najeriya,Bola Ahmed Tinubu ya ce za su ƙara tsaurara matakai domin kawo ƙarshen rashin tsaro.
Wannan dai na cikin wata sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai Bayo Onanuga ya fitar a ranar Lahadi 22 ga Maris 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da mataimakinsa da gwamnoni 23 a ranar Lahadi.
Tinubu ya jaddada cewa rashin tsaro na hana ci gaba da bunƙasar tattalin arziki, yana mai cewa an fara tattaunawa da wasu ƙasashe domin samar da kayan aiki da tallafi na zamani wajen yaki da matsalar.
Haka kuma, sanarwar ta nuna cewa shugaban ƙasar ya bukaci gwamnoni su ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma, tare da daukar matakan rage tasirin hauhawar farashi da rikicin Gabas ta Tsakiya ke haddasawa.