Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan hare-haren kunar baƙin wake da suka girgiza birnin Maiduguri.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya yi alhinin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 23 tare da jikkata sama da mutum 100, lamarin da ya bayyana a matsayin abin takaici da tayar da hankali.
Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna damuwarsa kan yadda hare-haren ke ci gaba da addabar jama’a, musamman a jihar Borno.
Kwankwaso ya ce:
“Na yi matuƙar baƙin ciki da waɗannan munanan hare-hare na kunar baƙin wake da suka afku a Maiduguri, wanda ya yi sanadin rasa rayukan mutane 23 marasa laifi tare da jikkata sama da 100.”
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu ke karɓar magani a asibitoci.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare na baya-bayan nan, haɗe da waɗanda suka gabata a Borno, na nuna yiwuwar sake dawowar barazanar ta’addanci a yankin.
Kwankwaso ya gargaɗi cewa wannan yanayi na iya kawo cikas ga zaman lafiya da aka shafe shekaru ana ƙoƙarin dawo da shi a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce:
“Wadannan hare-hare sun nuna wata barazana mai tayar da hankali na sake dawowar ta’addanci marar ma’ana, wanda ke barazana ga zaman lafiyar al’ummominmu. Ba za mu taɓa lamunta ba.”
Haka kuma, ya buƙaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ɗauki mataki a cikin gaggawa domin dakile matsalar tsaro.
A cewarsa, lokaci ya yi da za a bai wa jami’an tsaro cikakken iko da kayan aiki domin su iya fuskantar waɗannan barazana yadda ya kamata.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su haɗa kai wajen samar da goyon baya da kayan aikin da ake buƙata domin murkushe ‘yan ta’adda gaba ɗaya.
Kwankwaso ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da waɗanda suka jikkata, tare da daukacin al’ummar Borno, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan tare da bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.