Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump: Za mu tabbatar an buɗe mashigar Hormuz a kowane hali

Trump: Za mu tabbatar an buɗe mashigar Hormuz a kowane hali

Trump ya ce Amurka za ta ɗauki mataki domin buɗe mashigar Hormuz.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su buɗe mashigar Hormuz ko ta halin ƙaƙa don jirage su wuce cikin kwanciyar hankali.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce yana fatan China da Faransa da Japan da Koriya da Kudu da kuma Birtaniya za su aika jiragen ruwa na yaƙi zuwa mashigar ”domin kare duk wata barazana” daga Iran.

Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama za su aika jiragen ruwansu na yaƙi domin tabbatar da ”tsaro a mashigar”

Ya ce a yanzu Amurka za ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan jiragen ruwan Iran da ke wajen mashigar”.

Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta ”lalata kashi 100 na ƙarfin sojin Iran, amma ya ce takan yi amfani da jirage marasa matuƙa da dasa nakiyoyi da kuma makamai masu linzami masu cin gajeren zango.

Wakilin Iran a Geneva, Ali Bahrani ya ce iƙirarin Trump ɗin na lalata ƙarfin sojin Iran ”ƙirƙirarren labari ne”.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments