Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeBa mu da tabbacin za mu yi galaba a kan Iran –...

Ba mu da tabbacin za mu yi galaba a kan Iran – Isra’ila

Rahotanni sun ce Isra’ila ba ta da cikakken tabbacin cewa yaƙin zai kawo ƙarshen gwamnatin Iran.

Isra’ila ta bayyana shakku kan yiwuwar iya kawar da gwamnatin addini ta Iran sakamakon yaƙin da ƙasar ta Yahudu da kuma Amurka suka ƙaddamar kanta.

Kalaman na zuwa a dai-dai lokacin da Donald Trump ke cewa babu sauran wajen da ya rage basu kai wa hari a Tehran ba, a wani yanayi da sojojin na Washington ke duba yiwuwar fara kai hari kan tashoshin jiragen ruwan fararen hula.

Yanzu haka an shiga kwana na 13 da fara yaƙin Amurka da Isra’ila a kan Iran.

Wani ƙusa a gwamnatin ƙasar ta Yahudu a zantawarsa da Reuters ya ce har yanzu gwamnatin Malamai ta Tehran na da cikakken goyon baya jama’a, wanda ke nuna abu ne mai matuƙar wahala a iya kawar da gwamnatin ƙasar, duk da iƙirarin Banjamin Netanyahu da ke cewa yaƙinsu a ƙasar zai baiwa wayayyun Iraniyawa damar karɓar ragamar mulki.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da ganin ruwan makamai masu linzami daga Iran, waɗanda ke shafar yankuna da dama musamman birnin Tel Aviv fadar gwamnati, kodayake itama ƙasar ta Yahudu na ci gaba da ragargazar sassan Tehran, ciki har da harin da ta jikkata sabon jagoran addini na ƙasar, wato Ayatollahi Mojtaba Khamne’i.

Da ya ke tsokaci kan nasarorinsu a yaƙin da suka faro kan Iran, Donald Trump na Amurka ya ce a yanzu babu sauran wajen da basu farmaka a cikin ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba, kodayake ma’aikatar tsaron ƙasar ta bayyana yiwuwar kai hari wasu tashoshin jiragen ruwa na fararen hula waɗanda ta ce daga su ne dakarun na Iran ke kai hare-hare.

Sai dai cikin gaggawa Iran ta mayar da martanin cewa, muddin Amurkan ta kai hari tashoshin jiragen ruwan fararen hula a ƙasar to fa itama bazata yi ƙasa a gwiwa ba, domin zata mayar da martani ta hanyar kai makamancin harin.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta gargaɗi jama’arta an Iran da su kaucewa amfani da tashoshin jiragen ruwan domin su ne yankunan da sojojinta za su fara farmaka a yanzu.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments