Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya buƙaci gwamnatin tarayya, ta gaggauta shiga tsakani tare da ƙarfafa tallafin tsaro, biyo bayan wani ƙazamin hari da Ƴan bindiga suka kai a yankin Kafin Duguri, inda aka kashe mazauna garin tare da jikkata wasu.
Gwamnan, ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’umma, inda ya bayyana harin a matsayin wani babban ƙalubalen tsaro da ya mamaye cibiyoyin tsaro na yankin.
Ya ƙara da cewa, hukumomin tsaro a ƙasa suna buƙatar ƙarin nagartattun makamai da tallafin kayan aiki, domin tunkarar yan bindigar da suka mamaye sassan yankin.
Gwamnan ya bayyana hakan, yayin da yake wata ziyarar aiki an Abuja, inda ya yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bayanin halin da ake ciki.
A cewarsa, shugaban ƙasar a matsayinsa na babban kwamandan sojojin ƙasar, ya jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa tare da tabbatar wa al’ummar ƙasar goyon bayan gwamnatin tarayya, domin dawo da zaman lafiya.