Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeIsra'ila ce ke kan gaba wajen kisan ƴan jaridu - CPJ

Isra’ila ce ke kan gaba wajen kisan ƴan jaridu – CPJ

Kungiyar CPJ ta bayyana Iran a matsayin jagora wajen kashe yan jaridu

Ƙungiyar kare haƙƙin ƴan jaridu ta duniya CPJ ta ce Isra’ila ce ke da alhakin kashi 2 cikin 3 na kisan ƴan jaridar da aka yi a shekara ta 2025 da ta gabata.

Ƙungiyar CPJ ta ce shekarar 2025 ce wadda aka fi kashe ƴan jaridu fiye da kowane lokaci tun bayan fara aikinta shekaru fiye da 30 da suka gabata.

Ƙungiyar ta ce rikice-rikice da ke faruwa a duniya ya yi sanadin mutuwar ƴan jarida aƙalla 129, kuma 104 daga cikinsu Isra’ila ce ta kashe su a bara.

Duk da cewa adadin jami’an yaɗa labaran da ake kashewa a Ukraine da Sudan na ƙaruwa, amma mafi yawan waɗanda ke rasa rayukansu Falasdinawa da hare-haren Isra’ila a Gaza ke halakawa.

Rahotan da CPJ ta sabawa fitarwa a duk shekara kan adadin ƴan jaridun da ake kashewa ya bayyana cewa, shekarar 2025 ce ta biyu a jere da ƴan jaridar ke rasa rayukansu sakamakon yaƙin Gaza.

Haka zalika, CPJ ta ce Isra’ila ce keda alhakin kashi 81 cikin 100 na ƴan jarida 47 da aka kashe da gangan, tana mai cewa adadin ka iya ƙaruwa.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments