Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiTinubu ya nada Tunji Disu, a matsayin mukaddashin babban Sufeton yan sandan...

Tinubu ya nada Tunji Disu, a matsayin mukaddashin babban Sufeton yan sandan Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, bayan ya aike da takardar ajiye aikinsa bisa dalilai da suka shafi iyali.

Tinubu ya bayyana godiyarsa kan dogon lokaci da Egbetokun ya shafe yana hidimta wa rundunar ‘yan sanda da kasa baki daya, tare da yaba wa jajircewarsa da ƙwarewarsa wajen ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida tun bayan nadinsa a watan Yunin 2023.

Dangane da halin da tsaro ke ciki a kasar nan, Shugaba Tinubu ya amince da nadin Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu, a matsayin Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda nan takea cewar sanarwar Fadar Shugaban Ƙasar ta ranar Talata.

Sanarwar ta ce an yi naɗin ne bisa doka da shawarwarin shari’a, tare da bayyana cewa ƙwarewa da gogewar Disu za su taimaka wajen bai wa rundunar shugabanci mai ƙarfi a wannan lokaci mai muhimmanci.

Haka kuma, bisa tanadin Dokar ‘Yan Sanda ta 2020, Shugaban zai kira taron Majalisar ‘Yan Sanda ta Kasa domin duba nadin Disu a hukumance kafin a miƙa sunansa ga Majalisar Dattawa domin tabbatarwa.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments