Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa duk da hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran a bara, har yanzu ƙasar na ci gaba da shirye-shiryenta na nukiliya.
Trump ya ce gwamnatinsa ba ta samu wani tabbaci daga hukumomin Tehran da ke nuna cewa ba za su mallaki irin wannan makami ba.
Ya ƙara da cewa burinsa shi ne a warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, amma ya jaddada cewa ba zai taɓa bari abin da ya kira ƙasar da ta ke ta farko wajen daukar nauyin ta’addanci ta mallaki nukiliya ba.
Haka kuma ya zargi mahukuntan Iran da kashe aƙalla mutum dubu 32 yayin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati.