Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiYan ta’adda sun aika sakonnin gargadi kauyuka da dama a jihar Kwara

Yan ta’adda sun aika sakonnin gargadi kauyuka da dama a jihar Kwara

Yan ta’adda sun fara tura salon sakonnin gargadi zuwa wasu kyauyuka dake Jihar Kwara

Rahotanni sun ce a cikin kwanaki 6 da suka gabata, yan ta’addan sun aike da sakonni zuwa kauyuka 4 tare da barazanar kai musu farmaki daga yanzu zuwa kowane lokaci.

Manema labarai sun gano cewa, an ajiye wata wasika a kauyen Ira dake tsakanin Inaja da Aho a karamar hukumar Oyun.

Tun da fari dai yan bindigar sun tura wasikar gargadi ga kauyen Dunshigogo a karamar hukumar Kaiama, kwanaki kadan bayan harin ranar 3 ga watan Fabrairu a kauyen Woro wanda ya haddasa mutuwar mutum fiye da 176 da sace wasu 38.

Bugu da kari, bayanai sun ce mazauna Ira, Inaja da Aho sun fara yin hijira daga garuruwan nasu sakamakon barazanar da yan ta’addan ke yi.

Wani basarake a kauyen Ira, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce an ajiye wasikar ce a wata tashar babura dake kusa da babban masallacin kauyen.

SourceIconic FM
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments