Yayin da saura kwanaki kadan a fara azumin watan Ramadan, kasashe hudu sun riga sun bayyana ranar da za a ɗauki azumin farko.
Sun bayyana ranar bayan nazarin ilimin taurari da rahotannin hukumomin addini.
Rahotanni sun nuna cewa Oman, Turkiyya, Austalia da Singapore sun tabbatar da cewa za a fara azumin watan Ramadan ne a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026.
A cewar rahoton da aka wallafa a Gulf News, yawancin kasashen Musulmi za su nemi ganin jinjirin watan Ramadan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu.
Sai dai hasashen masana taurari ya nuna cewa hakan ba zai yiwu ba.
Ƙungiyar Masana Taurari ta Hadaddiyar Daular Larabawa (EAS) ta bayyana cewa za a haifi jinjirin watan ne a ranar Talata da misalin karfe 4:01 na yamma agogon UAE.
Shugaban kwamitin gudanarwar ƙungiyar, Ibrahim Al Jarwan, ya ce watan zai fadi ne minti guda kacal bayan faduwar rana a ranar Talata, lamarin da ke nufin ba za a iya ganinsa da ido ko da na’urar hangen nesa ba.
Saboda haka, ana sa ran Laraba, 18 ga Fabrairu, za ta kasance ranar karshe ta watan Sha’aban, yayin da za a fara azumi a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu.