Sunday, October 18, 2026
HomeLabarai'Yan Sandan Kano sun kama wani shahararren dan daba da ya addabi...

‘Yan Sandan Kano sun kama wani shahararren dan daba da ya addabi unguwar Dorayi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana yadda rundunar ta yi nasarar cafke wani gawurtaccen dan Daba mai suna Auwalu Ali wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, a ranar Litinin 2 ga Fabrairu 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa an cafke Auwalu Ali mai shekaru 26, wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, bayan samun sahihin bayanan sirri da ke nuna cewa yana hada tawagar ƴan daba domin kai hare-hare da sace-sace ga jama’ar Dorayi.

Sanarwar ta kara da cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bukaci al’umma su riƙa kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa domin ɗaukar matakin da ya dace.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments