Tsohon Ministan Shari’a na kasa kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, ya shigar da ƙara a gaban Kotu an Abuja, yana ƙalubalantar umarnin ƙwace masa wasu kadarori na wucin gadi da Hukumar EFCC ta samu.
A ranar 6 ga Janairu ne, Alƙalin Kotun Tarayya, Emeka Nwite, ya ba da umarnin ƙwace kadarori 57 da ake zargin an mallake su ne ta hanyar haramtattun ayyuka.
EFCC ta bayyana cewa kadarorin na da alaƙa da Malami da ’ya’yansa biyu, Abdulaziz Malami da Abiru Rahman Malami.
Yayin yanke hukunci kan ƙorafin da hukumar ta shigar ba tare da kiran ɓangaren Malami ba (ex parte), alƙalin ya ce akwai dalilai masu ƙarfi da ke nuna cewa kadarorin na da alaƙa da kuɗaɗen da ba su halatta ba, saboda haka yayi umarnin a ƙwace su na wucin-gadi tare da mayar da su hannun Gwamnatin Tarayya.
Har ila yau, kotun ta umarci EFCC da ta wallafa umarnin a jaridar ƙasa, tare da bai wa duk masu ruwa da tsaki kwanaki 14 su bayyana a kotu domin nuna dalilin da ya sa ba za a ƙwace kadarorin gaba ɗaya ba.
Sai dai Malami, ta hannun lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Joseph Daudu, ya ce EFCC ta samu umarnin kotu ne ta hanyar ɓoye muhimman bayanai da kuma gabatar da bayanan da ba su cika ba.
Daga cikin kadarorin da abin ya shafa akwai fili mai lamba 157 a Lamido Crescent, Nasarawa GRA, Kano, da aka saya a shekarar 2019, sai wani gidan bene a Wuse II, Abuja, wanda aka saya a shekarar 2018 kan kuɗi Naira miliyan 150.
Sauran kadarorin sun haɗa da Ginin ADC Kadi Malami Foundation, wanda rahotanni suka ce an saya kan Naira miliyan 56.