Rahotanni sun bayyana cewar duk da makonnin tattaunawa a baya-bayan nan, manyan shugabannin APC a matakin jihar Kano da na ƙasa sun ƙi amincewa da buƙatar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na garantin samun tikitin takarar gwamna kai tsaye a zaɓen 2027.
Majiyoyin da ke kusa da tattaunawar sun ce sharuɗɗan da ya bayar na sauya sheka sun haɗa da tabbacin tikitin takarar gwamna a 2027, haƙƙin zaɓar minista don wakiltar Jihar Kano a Majalisar Zartarwa ta Tarayya, da kuma ikon maye gurbin waɗanda aka naɗa a yanzu a Kano da masu biyayya gareshi.
Duk da haka, shugabannin APC sun ci gaba da dagewa cewa babu wata tattaunawa ta baya-bayan nan da za ta maye gurbin tsarin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Wani babban jigo a jam’iyyar APC a Arewa maso Yamma, wanda ya yi magana da Politics Digest bisa sharadin boye sunansa, ya ce jam’iyyar ba za ta yi watsi da ƙa’idodinta ga duk wanda ya sauya sheka ba.