Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta sanya lokacin yanke hukunci kan Tinubu bayan shigar da shi...

Kotu ta sanya lokacin yanke hukunci kan Tinubu bayan shigar da shi kara

Kotun Tarayya za ta yanke hukunci kan karar da aka shigar d Shugaban kasa Tinubu

Kotun Tarayya da ke Abuja ta saka ranar 9, Maris, 2026 domin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar kan ƙalubalantar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da dokar-ta-baci a Jihar Rivers.

Ƙarar dai ta shafi matakan da suka hada da ayyana dokar-ta-baci a jihar a shekarar 2025, ciki har da dakatar da zaɓaɓɓun shugabannin zartarwa da na majalisa da kuma kafa shugabanci na wucin-gadi.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya sake tayar da muhawara kan iyakar ikon shugaban ƙasa a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, musamman sashe na 305.

Mai shari’a James Omotosho ne ya ɗage sauraron shari’ar a ranar Juma’a bayan dukkan ɓangarori sun kammala gabatar da hujjoji kan sabon ƙudirin da aka shigar.

Ƙarar ta fito ne daga ƙungiyar CSOCLC, wadda ta shigar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Tarayyar Najeriya, Antoni-Janar na Tarayya, Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, INEC da kuma Gwamna Sir Siminalayi Fubara.

Kungiyar ta ce matakan da aka ɗauka bayan ayyana dokar-ta-baci sun saɓa wa kundin tsarin mulki.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments