Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wata ganawar sirri da Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke titin Miller Road ranar Talata.
Bayan ganawar ta, gwamnan ya isa zuwa Faransa a ranar Juma’a don ganawa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya nemi ganawa da Kwankwaso ne domin shawo kansa ya shiga jam’iyyar APC mai mulki, bisa abin da ake zargin umarnin shugaban ƙasa ne.
Majiyoyi dai sun bayyana cewa gwamnan ya isa gidan Kwankwaso ne da tsakar dare a wata mota ta musamman.