Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Isyaku Rabi’u, ya taya ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, murnar babbar nasarar da suka samu bayan doke ƙasar Algeria da ci 2–0.
Abdussamad Isyaku Rabi’u ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Facebook, inda ya ce nasarar ta ɗaga martabar Najeriya tare da faranta ran al’ummar ƙasa baki ɗaya, musamman yayin da ake shirin tunkarar wasannin daf da na ƙarshe (Semi-Finals).
A cikin sakon nasa, shugaban BUA ya yi alkawarin bayar da dala $500,000 ga ’yan wasan Super Eagles idan suka yi nasara a wasan daf da na ƙarshe, tare da ƙarin $50,000 kan kowace ƙwallo da za a zura.
Haka kuma, ya ce idan Super Eagles ta kai ga lashe wasan ƙarshe (Final), zai bayar da $1,000,000, tare da ƙarin $100,000 kan kowace ƙwallo da za a ci a wasan ƙarshe.
Ya ƙare sakonsa da yi wa tawagar fatan alheri da nasara, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da ɗaukaka sunan Najeriya a idon duniya.