Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce an samu tashin gobara 665 a sassan jihar daga ranar 1 ga Janairu zuwa 31 ga Disamba 2025.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis 1 ga Janairu 2026.
Sanarwar ta ce hukumar ta kai agajin gaggawa a kananan hukumomi 44 na jihar ta ofisoshi 30, inda aka karɓi kiran gaggawa da suka shafi gobara, ceto da kuma kiran ƙarya.
Sanarwar ta ƙara da cewa an gudanar da aikin ceto 130, yayin da aka samu kiran ƙarya 43 a cikin shekarar da ta gabata.
Game da asarar rayuka, sanarwar ta ce mutane 120 sun rasu sakamakon gobara, hatsurran mota da fadawa rijiyoyi da kududdufai, yayin da an ceto rayukan mutane 91.
Hukumar ta ce an yi hasashen asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 6.4, yayin da aka kiyasta kadarar dukiya da aka tsira da ita zuwa Naira biliyan 15.3.