Mambobin zartarwa na Jam’iyyar NNPP a Unguwar Gargari, Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano, sun kori tare da sallamar Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jiha, Hashimu Dungurawa, daga cikin jam’iyyar.
Jimillar mambobi 27 na zartarwar unguwar ne dai suka sanya hannu kan kudurin da ya amince da matakin, wanda aka cimma a yayin taron zartarwa na biyu na unguwar, da aka gudanar makonni biyu bayan babban zaɓe.
Taron dai ya gudana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Unguwar, Shuaibu Hassan, tare da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa.
A cewar kudurin, an sallami Dungurawa ne bisa zargin haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar, tayar da rikice-rikicen cikin gida, kasa biyan kuɗaɗen jam’iyya, da kuma yin kalaman cin mutunci ga Gwamnan Jihar Kano.
Sun ce an ɗauki matakin ne bisa bin ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, tare da jaddada muhimmancin kiyaye ladabi, haɗin kai da daidaito a cikin jam’iyyar.
Shugabancin unguwar ya bayyana cewa an tura kwafin kudurin zuwa ofisoshin jam’iyyar na Karamar Hukuma, Jiha da kuma na Ƙasa domin ɗaukar matakan da suka dace.
Haka kuma, an miƙa kudurin ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf,