Thursday, November 12, 2026
HomeLabaraiKano: kotu ta yanke wa mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda...

Kano: kotu ta yanke wa mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe yaro mai shekara 4

Babbar kotun jihar Kano da ke kan titin Miller Road ta yanke wa Hamisu Baita, wanda aka fi sani da Dan’umma Dandago, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe wani yaro mai suna Suyudi Suraj mai shekaru hudu.

Babbar kotun jihar Kano da ke kan titin Miller Road ta yanke wa Hamisu Baita, wanda aka fi sani da Dan’umma Dandago, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe wani yaro mai suna Suyudi Suraj mai shekaru hudu.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu shida da kuma hujjoji guda 12 da suka tabbatar da laifin wanda ake tuhuma.

Lamarin ya faru ne a shekarar 2023, lokacin da Baita ya shiga gidan iyalan yaron tare da daukarsa zuwa wani wajen zubar da shara tsakanin unguwannin Dandago da Sani Mai Nagge.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya kashe yaron tare da cire masa daya daga cikin idanunsa. Bayan faruwar lamarin ne jami’an tsaro suka kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Hukuncin kisan ya biyo bayan shari’a mai tsawo, inda kotun ta bayyana gamsuwarta da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar duk da kokarin da wanda ake tuhuma ya yi na kare kansa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments