Thursday, November 12, 2026
HomeLabaraiAna fargabar rikici ka iya raunana muradun Arewa

Ana fargabar rikici ka iya raunana muradun Arewa

Wani farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Kamilu Sani Fage, ya ce rikicin na iya raunana tasirin ACF da kuma ɓata sunanta a idon al’umma.

Wani farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Kamilu Sani Fage, ya ce rikicin na iya raunana tasirin ACF da kuma ɓata sunanta a idon al’umma.

Ya bayyana cewa ACF na cikin manyan ƙungiyoyin da ke fafutukar kare muradun Arewa, amma rikicin cikin gida na iya karkatar da hankalinta daga matsalolin da suka shafi yankin zuwa takaddamar shugabanci.

Shi ma wani masanin siyasa a Jami’ar Abuja, Farfesa Abubakar Kari, ya bayyana rikicin a matsayin gwagwarmayar neman iko da fa’idodin da ke tattare da mulki tsakanin manyan mutane, ba rikicin ƙabila ko addini ba.

Kari ya ce rikicin ya zo ne a lokacin da Arewa ke fuskantar matsalolin tsaro, talauci da sauran ƙalubale da ke buƙatar haɗin kai da shugabanci mai ƙarfi. Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da takaddamar na iya rage tasirin ƙungiyar tare da ƙara ɓata hoton yankin.

Ya buƙaci ɓangarorin da ke rikici da juna su sasanta tsakaninsu domin dawo da martabar ƙungiyar, yana mai cewa rikicin neman iko da kuɗi na iya jawo rugujewar kowace ƙungiya idan ba a magance shi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments