Sunday, November 8, 2026
HomeLabaraiOK Movement ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin kai wa...

OK Movement ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin kai wa magoya bayan NDC hari a Delta

Ƙungiyar Obi/Kwankwaso (OK Movement) ta buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin kai wa magoya bayan jam’iyyar NDC hari a yayin tattakin neman goyon baya na mutum miliyan ɗaya da suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Ƙungiyar Obi/Kwankwaso (OK Movement) ta buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin kai wa magoya bayan jam’iyyar NDC hari a yayin tattakin neman goyon baya na mutum miliyan ɗaya da suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Mai kula da ƙungiyar a jihar Delta, Favour Emerue, ne ya yi wannan kiran yayin wani taron manema labarai a ranar Asabar.

Emerue ya buƙaci a kama tare da gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a harin, ciki har da waɗanda ya ce sun ɗauki nauyin gudanar da shi.

Ya yi zargin cewa wasu ’yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa tattakin, inda suka kai wa mahalarta hari da sanduna, wuƙaƙe, adduna da sauran makamai masu haɗari.

Ya ce wasu magoya bayan jam’iyyar sun samu raunuka daban-daban kuma ana kula da su a asibitoci a faɗin jihar Delta, yayin da aka lalata motocin yaƙin neman zaɓe da dama na jam’iyyar.

Mai kula da ƙungiyar ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya da kuma take haƙƙin ’yan ƙasa na yin taro da haɗa kai bisa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ya yi zargin cewa yawan magoya bayan NDC da suka fito daga ƙananan hukumomi 25 na jihar Delta ne ya tayar da hankalin abokan hamayyarsu na siyasa, lamarin da ya ce ya kai ga amfani da tashin hankali.

Emerue ya buƙaci Gwamna Sheriff Oborevwori da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da adalci kan lamarin.

Ya kuma yi kira ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da su kamo waɗanda ke da hannu a harin, tare da tabbatar da tsaron ’yan siyasa yayin gudanar da kamfen.

Haka kuma, ya buƙaci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙungiyoyin farar hula, ’yan jarida da shugabannin addinai da su yi Allah-wadai da tashin hankalin siyasa.

Ya yi kira ga magoya bayan NDC da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar fansa, su bi hanyoyin doka wajen bayyana korafe-korafensu da zaɓin siyasa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jam’iyyar ADC ma ta koka kan jerin hare-haren da ta ce ake kai wa magoya bayanta a wannan lokacin yaƙin neman zaɓe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments