Saturday, November 7, 2026
HomeSiyasaBuhari ya yi alkawarin ba ni takarar shugaban Najeriya na APC a...

Buhari ya yi alkawarin ba ni takarar shugaban Najeriya na APC a 2022 – Amaechi

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi masa alkawarin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2022.

Amaechi ya ce ya rasa tikitin ne sakamakon bin shawarar da Buhari ya ba shi na kada ya fara kamfen kafin lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Mainland 98.3FM da ke Legas, ranar Juma’a.

A yayin hirar, ya yi tsokaci kan yadda ya fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen fidda gwani na APC a shekarar 2022, inda Tinubu ya samu nasarar lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments