Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 8 ga Disamba, 2026, domin yanke hukunci kan ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar yana neman diyyar Naira biliyan 10 daga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).
El-Rufai ya shigar da ƙarar ne bisa zargin cewa hukumar ta hana shi ganawa da matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, a lokacin da yake tsare a hannunta.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar ne a kan ICPC, shugabanta, Musa Aliyu, SAN, da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF).
A cikin ƙarar, El-Rufai na neman kotu ta ba shi diyyar Naira biliyan 10 bisa zargin tauye masa haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulkin ƙasar, musamman dangane da mu’amalarsa da iyalansa.
Sai dai batun ko zargin da tsohon gwamnan ya gabatar ya yi daidai da doka, da kuma ko zai samu diyyar da yake nema, na hannun kotu ne ta yanke hukunci.