Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya taɓa aiki a matsayin direban tasi da wasu ayyuka domin samun kuɗin biyan kuɗin karatunsa a Amurka.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, inda ya ce ya jinkirta fara karatu na wasu watanni domin tara kuɗin da zai biya.
Ya ce bayan komawarsa birnin Chicago, ya riƙa gudanar da ayyuka daban-daban domin biyan kuɗin makaranta da masauki, yana mai cewa ya san ƙalubalen da ɗalibai ke fuskanta wajen neman ilimi.
Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin faɗaɗa damar samun ilimi, inda ya bayyana cewa an bayar da rancen ɗalibai sama da naira biliyan 372 ta shirin NELFUND.
Ya kuma ce sama da mutane miliyan 2.8 sun nemi shiga shirin koyon sana’o’i da fasahohi, yayin da aka gyara kwalejojin fasaha 38 a faɗin ƙasar.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnati ta amince da ƙarin kashi 40 cikin 100 na albashin malaman jami’o’i, tare da ware naira biliyan 110 domin gyaran makarantun koyon aikin likitanci guda 24.