Friday, November 6, 2026
HomeKasashen wajeAbdul El-Sayed ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa sanata a...

Abdul El-Sayed ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa sanata a Amurka

Abdul El-Sayed, ɗan jam’iyyar Democrat, ya kafa tarihi bayan lashe zaɓen kujerar sanata mai wakiltar jihar Michigan a zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamba.

Abdul El-Sayed, ɗan jam’iyyar Democrat, ya kafa tarihi bayan lashe zaɓen kujerar sanata mai wakiltar jihar Michigan a zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamba.

Dan takarar mai shekara 42 ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican, Mike Rogers, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai kuma jami’in FBI.

Nasarar tasa ta sa ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa zuwa majalisar dattawan Amurka, duk da cewa Musulmai sun taɓa zama ’yan majalisar wakilai a ƙasar.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, El-Sayed ya mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa, faɗaɗa damar samun kiwon lafiya da rage tasirin attajirai da manyan kamfanoni a siyasa.

Kafin shiga siyasa, El-Sayed likita ne kuma ƙwararre a fannin nazarin cututtuka, sannan ya taɓa jagorantar hukumar lafiya ta birnin Detroit. A shekarar 2018 ya tsaya takarar gwamnan Michigan, amma bai samu tikitin jam’iyyar Democrat ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments