Jam’iyyar NNPP ta shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tana ƙalubalantar sauya shekar wasu ’yan majalisa da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen 2023.
A cewar jam’iyyar, ƙarar ta shafi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ’yan majalisar da suka sauya sheƙa, waɗanda suka haɗa da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano 28, ’yan Majalisar Wakilai 18 da sanatoci biyu.
NNPP ta yi zargin cewa waɗannan ’yan majalisa sun koma wasu jam’iyyu ba tare da bin matakan da suka dace na ficewa daga cikinta ba, duk da cewa har yanzu suna riƙe da kujerun da suka samu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin ’yan majalisar suka bayyana a jerin sunayen ’yan takarar wasu jam’iyyu na zaɓen 2027 da INEC ta fitar.
A cikin ƙarar, NNPP ta nemi kotun ta yi fassarar tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, musamman sassa na 68 da 109, waɗanda suka bayyana yanayin da ɗan majalisa zai iya rasa kujerarsa sakamakon sauya sheƙa.