Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiShugaban INEC ya ziyarci Sarkin Gombe domin tattauna batutuwan zaɓen 2027

Shugaban INEC ya ziyarci Sarkin Gombe domin tattauna batutuwan zaɓen 2027

Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya ba sa cikin kowace jam’iyyar siyasa, yana mai cewa wajibi ne su kasance masu adalci ga dukkan al’ummar da suke jagoranta.

Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya ba sa cikin kowace jam’iyyar siyasa, yana mai cewa wajibi ne su kasance masu adalci ga dukkan al’ummar da suke jagoranta.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, a fadarsa da ke Gombe.

Ziyarar na zuwa ne a yayin wani taron INEC da jami’an zaɓe da masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Gabas, domin tattauna shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027.

Abubuwan da aka tattauna sun haɗa da rawar da sarakunan gargajiya za su taka wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya, lumana da adalci.

Sarkin ya jaddada cewa bai kamata sarakuna su bari son zuciya ko bambancin siyasa ya raba kan al’ummomin da suke jagoranta ba. Ya ce aikinsu shi ne yi wa kowa hidima ba tare da la’akari da jam’iyya, addini ko matsayinsa a cikin al’umma ba.

Ya kuma bayyana cewa gudanar da zaɓe cikin ’yanci da lumana na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

A nasa ɓangaren, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya kai ziyarar ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da sarakunan gargajiya gabanin zaɓen 2027.

Hukumar ta yi imanin cewa sarakunan gargajiya za su iya taimakawa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaɓe, rage ƙin fitowa zaɓe, yaɗa sahihan bayanai da kuma hana tashin hankali a lokacin siyasa.

Ana ganin haɗin gwiwar INEC da sarakunan gargajiya na da muhimmanci wajen samar da yanayin da zai ba ’yan Najeriya damar gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da gaskiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments