Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta musanta kasancewa da hannu a shari’ar da ke kalubalantar takarar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, a zaɓen shekarar 2027.
Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 2 ga Nuwamba, 2026.
Doguwa ya ce zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa APC na da hannu a shari’ar ba shi da tushe, yana mai cewa rikicin ya samo asali ne daga cikin gida na jam’iyyar NDC, inda wasu mambobinta suka shigar da ƙara a kanta.
Ya jaddada cewa APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf da gwamnatin Jihar Kano ba su da hannu a shigar da ƙarar, kuma jam’iyyar ba ta yi wani tasiri kan yadda shari’ar ke gudana ba.
Shugaban APC ɗin ya ƙalubalanci Kwankwaso da ya gabatar da sahihiyar hujja da za ta tabbatar da zargin da yake yi, tare da bayyana cewa jam’iyyar tana mutunta ’yancin bangaren shari’a.
APC ta kuma jaddada cewa duk ɗan takarar da ya cika ƙa’idojin doka yana da ’yancin shiga zaɓen shekarar 2027.