Monday, October 19, 2026
HomeTsaroJami'an NSCDC sun yi batan dabo sakamakon harin ƴan bindiga a Neja

Jami’an NSCDC sun yi batan dabo sakamakon harin ƴan bindiga a Neja

Wasu daga cikin jami’an hukumar NSCDC sunyi batan Sabo bayan ƴan bindiga suka kai wa ofishin jami'an Rundunar hari

Wasu jami’an rundunar tsaro ta NSCDC sun ɓata bayan wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai wa wani ofishin jami’an rundunar a ƙauyen Ibrahim Leleh da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigar masu yawa da suka shiga ƙauyen sun buɗe wuta kan duk wnai jami’n tsaron da suka yi arab da shi da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Talata, al’amarin da ya tilasta wa jami’an NSCDC sun shiga daji domin tsira da rai.

Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ƴan bindigar sun ƙwace ƙauyen bayan ƙwace makaman jami’an rundunar.

Kakakin rundunar ta NSCDC a jihar Naija, Abubakar Rabi’u ya tabbatar wa da jaridar afkuwar al’amarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments