Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiSarkin musulmi ya cika shekaru 20 a kan karagar mulki

Sarkin musulmi ya cika shekaru 20 a kan karagar mulki

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulkin masarautar Sakkwato.

A cikin saƙon taya murnar da ya fitar, Gwamna Bago ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin shugaba mai tawali’u, haƙuri da tausayi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci da bunƙasa al’umma.

Gwamnan ya kuma yaba da rawar da Sarkin Musulmin ke takawa wajen inganta fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba.

Bago ya ce jagorancin Sarkin Musulmin ya bayar da muhimmiyar gudummawa ga addinin Musulunci, masarautun gargajiya da ci gaban Najeriya. Ya kuma roƙi Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima da basira domin ci gaba da jagorantar al’ummar Musulmi.

A nasa ɓangaren, Farfesa Isa Ali Pantami, wanda ke riƙe da sarautar Majidadin Daular Usmaniyya, ya taya Sarkin Musulmin murna, yana mai bayyana shekaru 20 na mulkinsa a matsayin na hikima, tawali’u da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Pantami ya kuma yaba da gudummawar da Sarkin Musulmin ke bayarwa wajen inganta ilimi, haɗin kan ƙasa, taimakon marasa galihu da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments