Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaZan dawo Kano da zaman don tara wa Tinubu kuri’a a 2027...

Zan dawo Kano da zaman don tara wa Tinubu kuri’a a 2027 – Yahaya Bello

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin shafe makonni biyu a jihar Kano domin tattara goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Bello ya ce a shirye yake ya koma Kano ya zauna a jihar na tsawon makonni biyu idan hakan ya zama dole, domin tabbatar da cewa Tinubu da Abba sun samu nasara a zaɓen mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani shirin wayar da kan al’ummar Yarbawa kan harkokin siyasa da ƙarfafa musu gwiwa, wanda gidauniyar ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Leke Abejide, ta shirya a Kano.

A wajen taron, tsohon gwamnan ya yi kira ga al’ummar Yarbawa da sauran al’ummomin da ba ’yan asalin Kano ba da su haɗa kai wajen mara wa jam’iyyar APC baya a zaɓen 2027.

Bello ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya faɗaɗa ƙoƙarin tattara goyon bayan jama’a fiye da jawabai na siyasa, ta hanyar shiga cikin ayyukan da za su taimaka wajen tabbatar da nasarar shugabannin biyu.

A wani ɓangare na taron, Bello ya bayyana cewa kuri’u kusan 500,000 da Tinubu ya samu a Kano a zaɓen 2023 ba su gamsar da shi ba, inda ya ce yana sa ran jihar za ta samar wa shugaban ƙasar kuri’u miliyan biyu ko fiye a zaɓen 2027.

Ya kuma buƙaci a tabbatar da cewa goyon bayan ya shafi sauran ’yan takarar APC a dukkan matakan zaɓe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments