Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiBabu mai cutar Ebola a Adamawa – NCDC

Babu mai cutar Ebola a Adamawa – NCDC

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da cewa mutanen biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Yola, jihar Adamawa, ba sa ɗauke da cutar, bayan gwaje-gwajen dakin bincike guda biyu sun nuna babu ita.

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da cewa mutanen biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Yola, jihar Adamawa, ba sa ɗauke da cutar, bayan gwaje-gwajen dakin bincike guda biyu sun nuna babu ita.

Daraktan hukumar, Dr. Jide Idris, ya bayyana cewa a halin yanzu babu wanda aka tabbatar ya kamu da cutar Ebola a jihar Adamawa. Ya ce an kai rahoton mutanen biyu ne da safiyar ranar 30 ga Oktoba, 2026, bayan sun nuna wasu alamomin da suka buƙaci ƙarin bincike.

Idris ya ce an killace mutanen tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace, kafin tattara samfurori domin gwajin cutar. Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Adamawa, musamman kwamishinan lafiya da tawagarsa, bisa gaggawar da suka yi wajen tunkarar lamarin.

Ya ƙara da cewa wanda aka tabbatar ya kamu da cutar a baya a Babban Birnin Tarayya, Abuja, shi ne kaɗai aka tabbatar da cutar Ebola a Najeriya. Daraktan ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da dogaro da sanarwar hukumomin lafiya.

Hukumar ta kuma shawarci duk wanda ya fara fama da zazzabi, matsananciyar kasala, ciwon kai, ciwon jiki, amai, gudawa ko zubar jini ba tare da wani dalili ba, musamman idan ya yi mu’amala da wanda ake zargi da cutar, da ya garzaya asibiti domin samun kulawar likitoci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments