Friday, November 6, 2026
HomeWasanniƊan wasan FC Tenerife, ya rasu a filin wasa

Ɗan wasan FC Tenerife, ya rasu a filin wasa

Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Tenerife, Jesús de Miguel, ya rasu yana da shekaru 30 bayan samun munanan raunuka sakamakon karo da mai tsaron ragar ƙungiyar Andorra, Jesús Owono, a yayin wani wasa da suka fafata a daren Litinin.

Lamarin ya faru ne lokacin da mai tsaron ragar Andorra, Owono, ya fito daga cikin raga domin ƙoƙarin tare ƙwallon da aka aika daga nesa, inda gwiwarsa ta bugi ƙirjin De Miguel.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa De Miguel ya faɗi ƙasa nan take cikin azaba, kafin daga bisani ya daina motsi. Hakan ya sa ’yan wasan ƙungiyoyin biyu suka garzaya domin kiran jami’an lafiya don kai masa ɗauki.

Duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto rayuwarsa, rahotanni sun tabbatar da rasuwar ɗan wasan mai shekaru 30 sakamakon raunukan da ya samu a karon.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments