Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaAna biyan mutane kuɗi domin sukar Tinubu a kafafen sada zumunta -...

Ana biyan mutane kuɗi domin sukar Tinubu a kafafen sada zumunta – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa ana biyan wasu mutane kuɗi domin su riƙa sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa a kafafen sada zumunta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Akpabio ya bayyana hakan ne lokacin da ƙungiyar matasan Arewa mai suna Arewa Revival Project, ƙarƙashin jagorancin Mustafa Ibrahim, ta kai masa ziyara tare da ba shi lambar yabo saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa.

A yayin ziyarar, Akpabio ya yi kira ga matasan Arewa da su ƙara wayar da kan jama’a a matakin ƙananan hukumomi domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, musamman sauye-sauyen haraji, yana mai cewa shugaban ƙasar na ƙoƙarin rage dogaro da man fetur wajen tafiyar da tattalin arzikin Najeriya.

Dangane da matsalar tsaro, Akpabio ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Ya kuma yi ikirarin cewa kusan jihohi 30 sun amince da gyaran kundin tsarin mulkin da zai ba da damar kafa rundunonin.

Ya bayyana fatansa cewa za a fara aiwatar da tsarin nan ba da jimawa ba, domin taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments