Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaINEC za ta fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027

INEC za ta fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar da za su fafata a babban zaɓen 2027 bayan kammala aikin sake dubawa da gyara kurakuran da aka samu.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Gombe, yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen wani taron tattaunawa da ma’aikatan hukumar daga yankin Arewa maso Gabas.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Amupitan ya ce an gudanar da bitar ne domin magance korafe-korafen da hukumar ta samu, ciki har da kurakuran rubutu a sunayen ’yan takara da kuma wasu batutuwan da suka shafi shari’o’in zaɓe guda biyu.

Ya ƙara da cewa hukumar ta ware wa’adin kwanaki 14 domin kammala aikin sake duba jerin sunayen kafin ta fitar da sabon jerin da aka gyara ga jama’a.

A cewarsa, INEC za ta sanar da sakamakon bitar nan ba da jimawa ba, sannan ta wallafa sabbin sunayen ’yan takarar da za su fafata a babban zaɓen shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments