Jami’ar Iconic Open University da Jami’ar Abuja sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin ilimi, horar da ɗalibai a aikace da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, a harabar Jami’ar Abuja, yayin wani taro da manyan jami’an cibiyoyin biyu suka halarta.
Tawagar Jami’ar Abuja ta samu jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi, tare da magatakarda, Malam Alkasim Musa Umar, da sauran manyan jami’an jami’ar.
A ɓangaren Iconic Open University kuwa, Farfesa J. U. Yahaya ne ya jagoranci tawagar a madadin mataimakin shugaban jami’ar. Tawagar ta haɗa da magatakarda, Muhammad G. Sanusi, da Dakta Peter Alabi, da sauran jami’ai.
Wannan yarjejeniya ta zo ne a daidai lokacin da jami’o’in Najeriya ke neman hanyoyin faɗaɗa damar samun ilimi mai inganci. A watan Satumban 2026, Iconic Open University ta samu cikakken lasisin gudanar da ayyukanta daga Gwamnatin Tarayya, wanda ya tabbatar da amincewar gwamnati da jami’ar.