Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kai ziyara ga Malam Ahmad Zakka da iyalansa bayan sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.
A yayin ziyarar da ya kai musu a gidan kulawa na gwamnatin jihar, gwamnan ya bayyana cewa iyalan na ci gaba da samun kulawar lafiya bayan an sallame su daga asibiti.
Uba Sani ya kuma yi alƙawarin tallafa wa iyalan domin taimaka musu wajen murmurewa da komawa rayuwarsu ta yau da kullum.