Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai halarci dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a faɗin ƙasar ba, yana mai cewa yana buƙatar mayar da hankali kan gudanar da mulki da kuma tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya jaddada cewa akwai buƙatar ya sauke nauyin da ke kansa na shugabancin ƙasa, musamman wajen kula da manufofin gwamnati da aiwatar da matakan da aka tsara domin inganta tattalin arzikin Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC ke shirin fara ayyukan yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.