Wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar ’yan ta’addan Lakurawa ne sun kashe sojojin Nijeriya biyu da wani ɗan ƙasar China a wani hari da suka kai kan ma’aikatan gine-gine a Ƙaramar Hukumar Maiyama ta Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sojojin da aka kashe suna ba da kariya ne ga ɗan ƙasar China da sauran ma’aikatan da ke aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.
A cewarsa, maharan sun kai harin ba-zata ne, inda suka kashe sojojin biyu da ɗan ƙasar China tare da jikkata wasu mutane.
Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun fara aikin neman waɗanda ake zargin sun kai harin.
A wani labarin kuma, rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta ce dakarunta sun daƙile wani hari da ake zargin Lakurawa ne suka kai wa sansanin soji da ke Maiyama da sanyin safiyar Laraba.
Jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya bayyana cewa maharan sun yi amfani da makamai daban-daban, ciki har da bindigar mai jigida da gurneti masu harba wa ta roka, amma dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa tare da tilasta musu ja da baya.
Danja ya ce a yayin bin diddigin maharan, dakarun sun ƙwato babura 17, bindigar mai jigida, bindiga samfurin AK-47, makamai da harsasai da kuma na’urar sadarwa.
Ya bayyana cewa wannan nasara ce da za ta rage ƙarfin ayyukan ƙungiyar a yankin.
Ya ƙara da cewa yankin na nan ƙarƙashin ikon dakarun tsaro, kuma ana ci gaba da sintiri domin gano sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a hare-haren.
Lamarin ya ƙara jawo hankali kan matsalar tsaro a yankunan da ke tsakanin jihohin Kebbi da Sokoto.