Fadar Shugaban Ƙasa ta ce jihohi hudu sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunar ’yan sanda ta jihohi.
Jihohin da suka amince da kudirin su ne Edo, Rivers, Osun da Oyo. Sai dai ana buƙatar amincewar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 kafin kudirin ya kai mataki na gaba.
Nnadubem Moghalu, babban mai taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tsare-tsare da bincike, ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro kan kafa ’yan sandan jihohi.
Ya ce gyaran kundin tsarin mulki da kudirin dokar ‘National Policing Bill’ matakai ne daban-daban amma masu alaƙa, inda gyaran kundin zai samar da tushen doka, yayin da dokar za ta tsara yadda tsarin zai gudana.
Moghalu ya ce ana buƙatar isasshen kuɗi, horo, kayan aiki da kyakkyawan tsarin jin daɗin jami’ai domin tabbatar da nasarar tsarin, yana mai cewa kafa ƙarin rundunoni kaɗai ba zai magance matsalolin tsaro ba.
Shi ma Sufeto-Janar na ’yan sanda, Olatunji Disu, ya ce rundunar tana goyon bayan matakan doka da kundin tsarin mulki da za su inganta aikin ’yan sanda da tsaron al’umma.