Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabarai2027: Jam’iyyun adawa na neman ɗan takara guda don fafatawa da Tinubu

2027: Jam’iyyun adawa na neman ɗan takara guda don fafatawa da Tinubu

Tattaunawa ta ƙara ƙamari domin haɗa kan jam’iyyun adawa a kan ɗan takara ɗaya da zai fafata da Tinubu

Shugabannin jam’iyyun adawa sun ƙara kaimi wajen ganin an samar da ɗan takara guda ɗaya da zai fafata da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A wani ɓangare na shawarwarin da ake ci gaba da yi, shugabannin wasu jam’iyyun adawa sun gana da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, a Abuja a daren Talata.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun tabbatar wa Daily Trust ta ce shugabannin sun tattauna kan abubuwan da ake buƙata domin samar da ɗan takara guda da kuma tabbatar da dorewar wannan tsari.

Majiyar ta ƙara da cewa shawarwarin ba su ƙare ba, kuma shugabannin jam’iyyun za su gana da sauran ‘yan takarar shugaban ƙasa a wani ɓangare na ƙoƙarin cimma matsaya guda.

Jam’iyyun da aka wakilta a taron sun haɗa da APM, PRP, wani ɓangare na PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, da SDP.

Majiyar ta ce har yanzu ana ci gaba da aikin, amma ta nuna cewa jam’iyyun da abin ya shafa suna duba yiwuwar mara wa ɗan takara guda baya.

A baya-bayan nan, ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce batun ɗan takara guda na ‘yan adawa zai kasance hannun jam’iyyun siyasa.

PRP ta tabbatar da faruwar ganawar a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Muhammed Ishaq, ya fitar jiya.

Jam’iyyar ta ce Atiku ya tarɓi ƙungiyar haɗin kan ‘yan adawa tare da ƙarfafa shugabanninta da su ci gaba da tafiyar da wannan yunƙuri gabanin babban zaɓen 2027.

PRP ta ce ganawar na daga cikin shawarwarin da ake ci gaba da yi tsakanin jam’iyyun adawa da shugabannin siyasa domin ƙarfafa haɗin gwiwa gabanin zaɓen.

A cewar sanarwar, Atiku ya nuna goyon baya ga ƙoƙarin tare da ƙarfafa shugabannin da su ci gaba da wannan tafiya.

PRP ta bayyana ganawar a matsayin “babbar hanyar ƙarfafa gwiwa” ga tawagar, inda ta ƙara da cewa ana shirin gudanar da wasu taruka da shugabannin sauran jam’iyyu da ‘yan takarar shugaban ƙasa.

Jam’iyyar ta ce shugabannin adawa sun fahimci buƙatar faɗaɗa da ƙarfafa haɗin gwiwar, yayin da shawarwarin siyasa ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen 2027.

Wannan ci gaba ya zo ne yayin da ƙungiyoyin adawa ke ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar haɗin gwiwa, yayin da Atiku shi ma ya nuna goyon baya ga ƙungiyar “Tinubu Must Go” bayan ya karɓi ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ta, Abba Hikima, a ranar Litinin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments